Nahiyar Afirka Zata Samu Karin Gurabu A Wasannin Cin Kofin Duniya

Ana sa ran nahiyar Afirka zata kara samun wasu gurabu har guda biyu a gasar wasannin cin kofin duniya da za’a gudanar a shekarar 2026, shugaban hukumar kwallon duniya Gianni Infantino, ne ya bada wannan tabbacin idan har an kara yawan kasashen da zasu fafata a wasannin gasar zuwa kasashe arba’in.

Yanzu haka kasashe talatin da biyu ne ke zuwa gasar, amma tun kafin zaben sa a watan fabarairu shugaban hukumar kwallon kafa na duniya ya bada shawarar cewa kara su zuwa arba’in zai yi tasiri matuka.

Yanzu haka dai nahiyar Afirka nada gurabu biyar ne a gasar, amma koda zancen Karin ya tabbata bazai soma aiki ba sai shekarar 2026.

A gasar kwallon kafa ta FA ta Ingila kuma za’a bada damar sauya ‘yan wasa har guda hudu a maimakon uku, a matakan karshe na gasar ta bana, kuma za’a soma sabon tsarin bayan amincewar hukumar kwallon kafa ta kasa da kasa. An gwada Karin ‘yan wasan zuwa hudu ne a gasar wasannin COPA America da aka gudanar a bana.