Shugaban Matasa masu kare martabar shugaba Muhammadu Buhari dake lardin arewacin kasar (Buhari Youth Vanguard) Honourable Abba Dala, ya bayyana cewa matakin gabatar da wasika ga ofishin shiyya na hukumar EFCC da takwararta ICPC dake jihar kano da wasu lauyoyin gwagwarmaya zasu gabatar a yau yayi dai dai.
Lauyoyin zasu mika wasikar ne akan bukatar kaddamar da bincike akan zargin mallakar gidaje a Dubai da aka yiwa babban hafsan sojin Najeriya laftanar janar Yusuf Tukur Buratai, ta hanyar amfani da kudaden haram, ya dace da abin da kungiyar su tasa a gaba.
Shugaban matasan ya ce, a matsayin sun a ‘yan kasa wadanda suka zabi wannan gwamnati, kuma suke bin shugaba Muhammadu Buhari, suna jawo hankalinsa akan cewa lallai ya kamata a matsayinsa na wanda duniya take girmamawa, ya dauki mataki akan lamarin.
Daya daga cikin lauyoyin ya bayyana cewa idan hukumomin basu dauki mataki akan bukatar tasu ba, to babu shakka zasu dauki matakin gurfananr dasu gaban kuliya.
Saurari cikakken rahoton a nan
Your browser doesn’t support HTML5