Tilas Ne ' Biyayya Ko Kuma Suyi Waje In Ji Mourinho

Jose Mourinho

Dan wasan Manchester United Anthony Martial, dan shekara ashirin ya bayyana rashin jin dadinsa bisa canja masa riga mai lamba tara zuwa lamba sha daya a kjungiyar ta Manchester United.

Martial,ya nuna bashib ransa ne ta kafa sada zumunta ta twitter inda yake sanyen da rigar Manchester United, mai lamba tara wanda ya saba sawa.

Makon da ya wuce ne sabon mai kula da kungiyar Jose Mourinho, ya gudanar da wamni garambawul na canja wa wasu ‘yan wasan lambar rigunar da suke sawa a kungiyar ta Manchester United, inda aka baiwa Martial, lamba goma sha daya sakamakon lamba tara da ya saba sawa, wanda aka baiwa Zlatan Ibrahimovic, sabon dan wasan Manchester United.

A gefe daya Jose Mourinho, yace tilas ne ‘yan wasan Manchester United, suyi mashi biyayya ko kuma su bar kungiyar.

Your browser doesn’t support HTML5

Tilas Ne ' Biyayya Ko Kuma Suyi Waje - 2'32"