Jirgin “SpaceX” Dauke Da Kaya, Ya Isa Tasha A Duniyar Wata!

Jirgin sarararin samaniya Space Station

Wani jirgi dauke da kayayyaki kirar “Space X” ya isa duniyar wata, jirgin ya sauka a tashar jiragen sama na kasa-da-kasa dake cikin sararrin samaniya. Cikin jerin masu gudanar da bincike a sararrin samaniya na kasar Amurka, Mr. Jeff Williams da Kate Rubins, sun yi amfani da mutunmutumin da aka kirkira don zuwa duniyar wata na kasar Canada, don sauke kayan dake cikin jirgin.

Cikin kayayyakin dake cikin jirgin akwai wani katafaren jirgi da zai dinga daukar mutane da kayan su, daga wani guri zuwa wani duk a cikin sararrin samaniya. Ana dai sa ran idan Allah, ya kaimu shekara mai zuwa ne za’a fara amfani da wannan jirkin.

Kamfanin da suka kirkiri jirgin SpaceX tare da haddin gwiwa da kamfanin Boeing, zasu fara kokarin ganin sun hada duk wasu kaya da ake bukata a sararin samaniya don koda akwai bukatar amfani jirgin wajen samar da tsaro ga kasashen duniya.