An Hallaka Matasa Biyu Cikin Masu Zanga Zanga A Bokkos Jihar Filato

A ijya ne Gwamnatin jihar Filato ta kaddamar da dokar hana zirga zirga ta awoyi 24 a karamar hukumar Bokkos dake jihar, a sakamakon zangazangar da matasan yankin suka yi ta nuna bakin cikin su akan kisan basarake mai suna Sar Ron Kulere, Dah Lazarus Agai, da wasu ‘yan ta’adda da ake zargin Fulani ne suka yi.

Wannan ya biyo bayan umurnin da babban sufeton ‘yan sanda yayi na tura mataimakin sa domin tabbatar da kama wadanda ake zargi da aikata kisan basaraken wanda aka hallaka tare matarsa da dansa da kuma jami’in dan sandan dake tare da shi.

An hallak basarakenne a ranar litini data gabata, lamarin da ya haifar da zanga zangar kungiyoyin matasa daga lunguna daban daban na yankin. Rahotanni sun bayyana cewa zanga zangar ta kaiga wani yanayi da jami’an tsaro suka bude wuta har suka hallaka wasu matasa biyu daga ciki.