WASHINGTON D.C —
Wani matashi ya auna arziki da ya sami kubuta daga hannun masu satar mutane a Obu Brach, Otukpa dake karamar hukumar Ogbadibo a jihar Benue.
Rahotoni na nuni da cewa wani mutun ne ya yaudari wani dan kabu kabu ko kuma dan okada zuwa cikin wani daji a kauyen Owoso, da niyyar sace shi.
Wani da aka yi abin a idon sa mai suna Daniel, ya ce wanda ake kokarin sace wan ne da dai yaga cewar bai gane ba sai ya doka ihu, abinda ya jawo hankalin manoma dake gonakinsu acikin dajin suka kawo dauki, inda shi kuwa mutumin ya ranta ana kare.
Kimanin makoni biyu da suka wuce wani mutun ya yaudari wani mai Okada zuwa daji inda ya aikata masa aika aika ya kuma haka rami ya rufe gawarsa.