An Yi Bukin Tunawa Da Tsohon Shugaban Afirka Ta Kudu Nelson Mandela

A cikin watan nuwambar shekarar 2009 ne taron kolin majalisar dinkin duniya ya amince da ayyana kowacce ranar 18, ga watan yulin kowace shekarata kasance ranar tunawa da shugaban afirka ta kudu marigayi Nelson Mandela domin irin gudummuwar da ya bayar wajan wanzar da akidar zaman lafiya da ‘yancin bil’adama a duniya.

Nelson Mandela wanda ya rasu yana da shekaru 67, ya shafe shekarun rayuwarsa yana hidima ga al’umma, musamman a matsayinsa na lauyan kare hakkin bil’adama, tsohon dan hursuna kuma mai fafutukar wazar da zaman lafiya, kana shugaban Afdirka ta kudu na farko a demokaradiyya bayan kawo karshen wariyar launin fata a kasar.

La’akari da rawar da ya taka ta fuskar ‘yancin bil’adama, yafiya da kawo daidaito a tsakanin al’ummar kasar, zauren na majalisar dinkin duniya ya fadada ranar tunawa da Mandela ta kunshi ayyukan jinkai da tausayawa al’umma musamman hursunoni da kuma wayar da kan jama’a akan muhimmancin ma’aikatan kurkuku.