Za'a Samarwa Matasa 10,000 Aikin Yi

Ismaila N'abba Afakallah

shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Isma’ila Na’abba Afakallah, ya ce gwamnatin tarayyar da hadin guiwar gwamnatin kano zasu samar da wani katafaren dandalin shirya fina finai a jihar Kano, wato Film Village a garin Kofa dake karamar hukumar Bebeji wanda za’a fara ginin a karshen wannan watan na Yulin.

Dandalin zai kasance na farko a Nijeriya, kuma na biyu a Afirka, wanda zai rika karbar baki masu shirya fina-finai daga kowacce kusurwa ta duniya da zasu yi amfani da dandalin don yin fina-finansu.

Za’a kashe fiye da Naira biliyan 3, wajen gina wannan katafaren dandalin wanda kuma ake sa ran cewa zai karbi bakuncin masu harkar fina finai daga koina afadin duniya.

Ana kuma sa ransa kammala aikin akan lokaci kuma zai samawar matasa kimanin 10,000 aikin yi.

Shugaban hukumar ya kara da cewa wannan dandali shine irinsa na biyu a Afirka bayan na Afirka ta kudu kuma gina wannan dandali zai kara kawo gogaiya tsakanin ‘yan film din Najeriya da na sauran duniya.

Your browser doesn’t support HTML5

Za'a Samarwa Matasa 10,000 Aikin Yi - 4'45"