Henrik Stenso Ya Kafa Gagarumin Tarihi A Wasan Golf

A jiya Lahadi ne Henrik Stenson ‘dan asalin kasar Sweden ya lashe gasar wasan golf da akayi a Scotland, a wani wasan da ba a taba ganin irin sa ba.

Stenson ya lashe bugun karshe na zagayen takwas na wasan, inda ya buge Ba-Amurken nan Phil Mickelson da bugu uku.

Wannan ya sa adadin cin da Stenson ya yi a gasar ya kai 264, ya yin da ya zama namiji na farko dan kasar Sweden da ya taba cin wata babbar gaza.