FIFA Zata Karawa Najeriya Kudaden Bunkasa Kwallon Kafa

Shugaban FIFA Gianni Infantino

Hukumar kwallon kafa ta duniya watau, FIFA, zata kara yawan kudaden da take baiwa Najeriya, domin habaka wasan kwallon kafa a kasar.

Rahoton hukumar ta FIFA, na nuni da cewa Najeriya, da sauran kasashen zasu sami karin dala Amurka miliyan biyar a cikin shekaru hudu.

Wannan na nuni da cewa kasashen zasu sami dala $750,000 a duk shekara, kudaden zasu kasance na samar da filayen wasanni, shirya gasar tsakanin kungiyoyi da ciyar da wasan kwallon kafar mata gaba.

Hukumomin wasan kwallon kafa na nahiyoyi zasu sami dala miliyan $40 aduk shekara wanda yake nuni da Karin miliyan $18.