Ranar 15, ga watan yuli na kowace shekara ranar ce da majalisar dinkin duniya ta ware domi bita da nuna mahimmancin koyawa matasa sanao’in hannu domin dogaro da kai, a wannan shekarar ma ba’a yi fashi ba ga wakilin mu Babangida Jibril da wasu daga cikin irin wadnnan matasa.
Taken bikin na bana dai shine koyar da sanao’i, domin samarwa matasa aiyukan yi, a duk shekara abinda majalisar dinkin duniya, tace zai taimakawa wajan tabbatar da tsaro domin kuwa zai baiwa irin wadanna matasa da ake amfani dasu wajen tashe tashen hankula sanao’in yi ta yarda hankulansu ba zai kai ga aikata aika aika ba.
A sakon sa domin wannan biki dai na bana babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon, ya jaddada kudirin majalisar dinkin duniya da kuma sauran kasashen duniya na saka jari da kuma koyawa matasa sanao’in hannu domin su kasance masu dogaro da kai matakin da yace zai taimaka wajan wanzar da zaman lafiya da kuma ci gaban al’uma da kare hkkin bil-Adama, kama daga Gwamnatin kananan hukumoni zuwa na tarayya, har ma da kungiyoyi da al’umomi masu zaman kansu.
Yanzu haka ana ci gaba da bude wurare tare da koyar da sanao’i, hannu ga dinbin matasan da ake dasu.
Samarwa matasa aiyukan yi dai masamma ma na hannu na daya daga cikin manfofin Majalisar dinkin duniya a kudirin ta na ci gaban al’uma da ake kira “Sustainable Development Goal” kafin nan da shekara ta 2030.
Your browser doesn’t support HTML5