An Sako Yunusa Yellow Daga Bayelsa Ya Dawo Gida Kano

Yunusa Dahiru Yellow

A yau shirin namu na mussamam ne domin kuwa Yunusa Dahiru wanda aka fi sani da Yellow ya dawo gida Kano bayan dogon badakalar da gwagwarmayar da ya sha shi da Ese Oruru.

Hukumomi a jihar Bayelsa, ne sun sako Yunusa Dahiru, bayan da ya kwashe tsawon lokaci a gidan yarin jihar wanda aka tsare a gidan yari a jihar ta Bayelsa, a bisa zargin sa da ake yi cewa ya sace Ese ya gudu da ita Kano.

Kotu dai ta bada belin Yunusa kuma tuni ya dawo gida Kano, inda Dandali ya samu zantawa da shi a garinsu dake Kura.

Yunusa ya ce ba shakka yayi darasi na rayuwa inda yake godewa mutanen da suka jajirce na ganin an sako shi daga kurkuku.

A can baya tsohon sufeton ‘yan Sanda Solomon Arase, ya bayana cewa Ese, na zaune ne a jihar Kano tun watan Agusta 2015, wanda tuni mahaifin Yunusa ya nuna rashin yardar sa ga soyayyar.

Yunusa yace ya fuskanci kalubale iri iri inda suke zagin shi da kuma kalaman cewa shi ya sace masu ‘yar uwa da makamatansu da kuma cewa ya sata shiga addini Musulunci, amma daga baya da masu kareshi suka sa baki shine ya sami sa’ida,Yunusa dai yace ya koyi darasi na rayuwa.

Shi kuwa mahaifin Yunusa cewa yayi farin ciki sosai, kuma anyi masa abinda har ya bar duniya bazaimata ba.

Your browser doesn’t support HTML5

An Sako Yunusa Yellow Daga Bayelsa Ya Dawo Gida Kano - 4'49"