Satar mutane domin neman kudin fansa ya zama ruwan dare gama duniya a sassa daban daban na Najeriya yanayin da ke bata sunan kasar a idon duniya da kuma haifar da matsalolin tattalin arziki musamman saka masu shi’awar zuba jari a kasar cikin fargaba.
Baya ga kudancin Najeriya inda matsalar ta samo asali, yanzu haka matsalar ta bazu har a arewacin kasar kama daga jihohin Adamawa da Taraba, da Bauchi, da Kano, da jihar Kaduna da Zamfara harma da Sokoto duk a arewacin kasar, lamarin dake jefa mazauna yankin cikin fargaba.
Dr Bawa Abdullahi Wase masani akan harkokin tsaro ya bayyana cewa akwai illoli da satar mutane domin nemen kudin fansa ke haifarwa kamar matsalar huldar jakadanci tsakanin kasa da kasa domin babu kasar da zataso ta tura jama’anta zuwa wata kasa da za’a sace su kamar yadda ya faru a Najeriya yayin da aka sace wani dan kasar Faransa.
Na biyu kuma shine masu zuwa saka jari daga wata kasa baza su so zuwa kasar da za’a sace su kokuma jefa rayuwarsu cikin hatsari ba kamar yadda da dama suka rasa rayukansu a Najeriya. Illa ta uku kuma itace haifar da rashin zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Babban kalubalen shine yadda ake samun matasa ‘yan sakandire dana gaba da makarantun sakandire cikin wannan mummunar aika aika.
Ga cikakken rahoton.
Your browser doesn’t support HTML5