Ghana Na Fuskantar Kalubalen Zuwa Olympic

Ghana Olympic

Sauran ‘yan makwanni Ghana ta shiga wasannin Olympic na wannan karon, koda yake kasar na huskantar matsalolin kudi da zata shiga wasannin.

‘Yan wasannin daban daban a fadin duniya zasu nufi birnin Rio na kasar Brazil don fara wannan babban wasa na kasa da kasa a ranar 5, ga watan Agusta 2016, zuwa ranar 21 ga watan Agustan shekarar 2016, Ghana zata fafata a fannoni kamar gudun tsere, ninkaya, damben boxing, kokawar judo da kuma daukar nauyi.

Koda yake ministan Matasa da Wasanni Edwin Nii Lantey Vanderpuye yace yana huskantar babban matsala wurin gano hanayar da kasar zata samo kudaden da zata nufi Brazil.

Ministan yace ko shakka babu akwai babban kalubale saboda kasar na bukatar kudade da zasu kai kusan dalar Amurka $230,000, kafin ta iya shiga wasannin Olympic.

Yace koda yake Ghana bata yi nasarar shiga wasannin kwallon kafa na maza da mata ba, amma dai zata fafata da kasashe a wasu humimman wasanni kamar gudun tsere, ninkaya, damben boxing, kokawar judo da kuma daukar nauyi.