Sabon manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, yayi watsi da hasashen da wasu masana tamaula keyi cewa wata sabuwar tsamar zata kunno kai a tsakaninsa da Jose Mourinho, wanda shi ma a kakar kwallo ta bana ya zamo sabon manajan daya kungiyar kwallon ta Manchester, watau United.
Masana tamaula sun ce manajojin biyu zasu sake sabunta wannan tsama ta su a fagen Firimiya Lig ta Ingila, a bayan da suka yi ta tsama a baya a kasar Spain, lokacin Guardiola yana koyar da FC Barcelona shi kuma Mourinho yana koyar da Real Madrid.
A jawabinsa na farko gaban ‘yan jarida tun bayan nada shi manajan Manchester City, Guardiola yace, “Ai Jose ya bayyana wannan lamarin daidai a lokacin da yace wannan lamarin fa ba wai a kansa ne ko a kai na ba.”
Ya ci gaba da cewa, “daga nesa abinda na hango shine cewa yana da wuya mutum ya lashe Wasanni a wannan lig na Firimiya.”
Da aka tambaye shi ko kungiyoyi nawa suka yi zawarcinsa daga Ingila, sai yace, “wannan kungiyar ce kawai don haka a koyaushe ina godiya sosai ga mutanen da suka amince da ni suka damka mini amana don in taho wannan kasa in koyar a Firimiya Lig.”
Yace ko ba dade ko ba jima, tilas ne kwach ya nuna irin kwazonsa a wasannin Firimiya Lig. Manchester City ta ba ni wannan dama kuma a koyaushe zan kasasnce mai godiya. Zan yi bakin kokari na domin in ga mun cimma gurorinmu, in ji Guardiola.
Your browser doesn’t support HTML5