Shahararren dan wasan kwallon kafar nan Lionel Messi da mahaifinsa sunce zasu daukaka kara akan hukuncin da wata kotu a kasar Spain ta yanke masu na daurin watanni 21 a sakamakon kama su da laifin coge wajan biyan kudin haraji a kasar.
Kotun dai taci Messi tarar kudi Euro miliyan biyu, yayin da mahaifin nasa kuma kotun ta ci shi tarar Euro milyan daya da rabi, bisa laifin yaudarar kasar da cogen kudi Euro miliyan hudu da dubu dari daya a shekarar 2007 zuwa 2009.
An bayyana tsohon dan wasan tsakiya na kasar Holand Clarence Seedorf a matsayin sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar Sin, Seedorf ya ta taba horas da ‘yan wasa a kungiyar AC Milan wacce ya bari a watan janairun shekarar 2014, bayan ya kwashe tsawon watanni biyar kacal.
Sai dai anyi ta alakanta shi da komawa kungiyar Newcastle da QPR a bara, Seedorf ya kasance dan wasa na farko a tarihi daya taba blashe kofin zakarun turai da kungiyoyi uku.