A wasan da aka buga a gasar nahiyar Turai a jiya tsakanin Portugal da Wales, an tashi wasan inda Portugal ta lallasa Wales, da kwallaye biyu da nema, a karshe a gasar kofin nahiyar yankin Turai, wanda ake yi a kasar Faransa.
Wannan shine karo na biyar da kungiyar kwallon kafa Portugal ta taba zuwa wanna matakin na kusa da na karshe wato (semi final).
Wanna dama da Portugal, ta samu ya bata damar kawowa wasan karshe kuma shine karo na biyu da kasar Portugal, din ta taba zuwa wasan karshe a gasar nahiyar Turai, inda ta buga a gasar 2004, da kungiyar kwallon kafa ta Greece, inda aka doke Portugal, da kwallo daya da nema.
Sai kuma wannan karon da kungiyar kwallon kafa ta Portugal, take jiran wasan karshe tsakanin ta da kungiyar kwallon kafar Jamus ko na Faransa wanda za’a buga wasan a yau da misalin karfe 8. Na dare agogon Najeriya, Nijar da Kamaru.
Your browser doesn’t support HTML5