An Dora Laifin Harin Da Aka Kaiwa Iraqi Akan 'Yan Siyasa, Jami’an Tsaro Da Ma’aikatar Jakadanci

Harin mamayen da sojojin kwanance na Amirka da Britaniya suka kai kasar Iraq shekaru goma sha uku da suka shige, bai zama wajibi ba, domin tsohon shugaban Iraq mai mulkin kama karya, marigayi Saddan Hussein ba ya jawowa Britaniya da giggan kasashen duniya wata barazana. Wannan bayani yana kunshe ne cikin rahoton rawar da Ingila ta taka a yakin da aka dade ana jira.

Bincike karkashin jagorancin wani tsohon ma’aikacin gwamnatin Ingila mai suna John Chilcat ya dora laifin shiga yakin da britaniya tayi akan yan siyasa da jami’an tsaro da ma’aikatan jakadanci da kuma manyan jami’an soja a saboda rawar da suka taka wajen kai harin mamaye a Iraq.

A wajen wani taron yan jarida daya cika makil da mutane a birnin London Mr Chilcat yace shirya kai karin mamaye yana cike da kura kura kuma an samu matsala ko kuma matsaloli wadanda har kwanan gobe ana fama da su.

Yace sun tantance cewa Britaniya tayi zabin shiga yakin, tun kafin ayi amfani da wasu hanyoyi kwance damar yaki cikin lumana.

An share shekaru bakwai ana gudanar da wannan bincike.

A yayinda aka gabatar da sakamakon wannan bincike. Kusan shekaru goma ke nan da aka kashe tsohon shugaban Iraq ta hanyar rataye shi. Jiya Talata dan takara shugaban na jam’iyar Republican Donald Trump ya yabawa salon mulkin marigayi Saddam Hussein. Donald Trump yace kodayake ana daukar Saddam Hussein a zaman mutumin da bashi da kirki, to amma kuma akwai abinda yayi da ya isa yabo. Yace Saddam Hussein yayi ta kashe ‘yan ta’ada a zamanin sa, bai bari sunyi sakat ba.

A saboda haka yace yakin da Amirka ta kaddamar a Iraq, kuskure ne. Mr Trump yace sha nanata wannan furuci, a saboda haka ya kamata tsohon shugaba Bush da shugaba Obama su nemi gafarar kaddamar da yakin.