Tabbatar Da Cikakken Tsaro A Lokacin Bukukuwan Sallah

Babbam kwamandan jami’an tsaron farin kaya da aka fi sani da Civil Defence Abdullahi Gana Muhammad ya bada sanarawar tura jami’an ma’aikata guda dunu arba’in domin gudanar da ayyukan hadahadar bukuwan sallah.

Kwamandan wanda yayi jawabinne a ranar asabar yayin da yke buda baki tare da wasu ‘yan jarida a gidansa dake birnin tarayya. Ya kuma yi Allah wadai da irin ta’asar da kungiyoyin masu tada kayar baya a kudancin kasar ke yi.

Mujallar Vanguard ta wallafa cewa kwamandan ya ce hukumar sa ta tura jami’ai dubu arba’in domin tabbatar da kare kaddarorin kasa a lokacin da ake gudanar da bukukuwan salla. Ya kuma umurci dukkan kwamandojin jahohi dasu sa ido wajan tabbatar da tsaro a dukkan wuraren dake karkashinsu.

Daga karshe ya bayyana cewa baza su yi kasa a gwiwa ba wajan tabbatar da tsaro, inda ya ce zasu yi aiki tare da sauran takwarorin su kuma dole ne a tura jami’ai sako-sako da lungu-lungu da ake zargi, da kuma wuraren da za’a gudanar da salloli, da kasuwanni, da manayan kantuna da kuma tashoshin mota.