Dokar Hana Tallace Tallace A Gefen Hanyoyin Jihar Legas Ta Fara Aiki Gadan Gadan

Da alamu umurnin da gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode ya bada na haramta tallace tallace a kai da gefen hanyoyi a fadin birnin ta fara aiki a sakamakon kasancewar kauracewa manyan tituna da hanyoyi da masu sayar da kayayyakin sukai domin tsoron kamu daga jami’an tsaro.

Wannan ya biyo bayan alwashin da jami’an tsaron jihar Legas suka yi na cewar zasu kaddamar da doka akan duk wanda suka kama yana talla a gefen hanya kamar yadda gwamnan jihar ya umurce su suyi.

A karshen makon nan ne gwamnan jihar Legas Ambode yaba jami’an tsaron jihar umurnin kama duk wani mai sayar da kaya a gefen hanya ko yawon talla akan manyan hanyoyi daga 1 ga watan Yulin wannan shekarar, cewa dokar hana tallar zata fara cikakken aiki daga wannan rana.

Gwamnan yayi Magana a wata hira ta akwatin talabijin inda ya bayyana cewa sabunta dokar nada nasaba da dokar jihar ta shekarar 2003, sashe na 1 akan dokar data haramta saye da sayar da kayayyaki a gefen tituna ba bisa ka’ida ba, kuma dokar ta haramta wannan a duk fadin jihar ta Legas.

Koda shike bisa rahoton masu saka idanu akan al’amurran sun bayyana cewa masu talla aka manyan hanyoyin sun kauracewa duka hanyoyin saidai kuma sun sake sabon salon tallata kayan nasu. Rahotannin sun bayyana cewa anga wasu daga cikin masu sayar da kayan jefi jefi akan titin Oshodi, da Egbeda,da Ikeja, da Ojo da kuma suran wurare.

Rayuwar Matasa A Life-Junction A Najeriya

Rahotannin sun kara da cewa masu sayar da kayayyakin sun bayyana bacin ransu da cewar gwamnatin jihar ta yi haka ne kawai domin ta kuntata masu da kuma jefa su cikin mawuyacin halin rayuwa da kuma sa dama kan hanyar aikata miyagun laifuka.