Neymar Zama Daram A Barcelona

Neymar mai shekaru 24 da haifuwa ya kawo karshen jita jita da ake yadawa zai ci gaba da wasansa da babban kungiyar Spain shekaru uku nan gaba awannan kakar wasa

Neymar ya sanya hannu akan kwantragin shekaru biyar da Club din Barcelona, zai ci gaba da yi mata wasa zuwa 2021

Kudin sabon kwantragin dan wasan kasar Brazil ya kai Euro miliyon 200 wanda yayi daidai da dollar Amurka miliyan 222.5, wanda kudin zai karu a sabuwar shekara zuwa euro miliyan 250 bisa wannan sabon yarjejeniyar.

Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeau, shine ya bayyana wannan labarin awani taron manema labarai aranar Alhamis alokacin da aka kammala shirya wannan yarjejeniya da dan shekaru 24 bayan ya bayyana amincewarsa da ci gaba da yin wasa da Barcelona

Neymar da yake shirin yi wa kasarsa ta Brazil awasannin Olympic sabuwar wata, an yi masa tunanin zai koma da wasa a kungiyoyi kamar Manchester United da Paris Saint-Germain amma sai gashi ya kara shekaru ukua club dinsa.

Aranar 15 ga watan Yuli ne za a mikawa Neymar takardun yarjejenyar a hukumance kafin wasannin Olympic.

Neymar ya zura kwallaye 85 awasanni 141 tun lokacin da ya koma Barcelona a shekarar 2013, yayi nasarar daukar kofina takwas ciki har da na league din La Liga sau biyu da kofin Champions league sau daya.