Hukuncin da alkalin babbar kotun birnin Abuja, Justice Valentine Ashi, ya yanke dake soke hanyar da PDP, ta biyo domin cike gurbin shugabancin ta da Sanata Madu Shariff, dan cike gurbin Ahmed Mu’azu, bai kawo karshen takaddamar PDP, ba.
Wannan dai saboda wata shari’a da babbar kotun tarayya zata yanke ranar 4, ga yuli, nan kan hallarcin cio gaba da mulkin Shariff, ko kuma saukar sa daga mukami.
Take kakakin Shariff din Inuwa, yace babu ma abinda ya hada su da hukuncin kotun Abuja, domin bada Shariff, ake Magana ba.
Kasalika an samu wata barakar ma inda shugabanin jihohi na PDP, ke bada labara mai cin karo da juna wasu na mara baya ga shugabbancin riko na Ahmed Makarfi, wasu kuwa na cewa a’a su suna tare da Shariff.
Tsohon mai taimakawa shugaba Jonathan Ahmed Gulak, shi ya kai karar da ta yi sanadiyar cike gurbin da Shariff ya hau mukamin da hakkan ya kawo karshen dogon rikon kwarya na Uche Secondus.
A yanzu dai ba daya daga cikin bangarorin biyu dake da ta gomashin amfani da hedkwatan dake Wadata plaza.
Your browser doesn’t support HTML5