Wasu kungiyoyin jinkai karkashin kungiyar Izala, sun ba marayu da matan da suka rasa mazajensu tallafi da kuma daukar dawainiyar karatun yara marayun domin taimakawa rayuwarsu dan kaucewa gararamba kan tituna.
Alhaji sa’idu Musa Yalwa shine shugaban kwamitin marayu na babban birnin tarayya kuma ya bayyana cewa abinda Allaha yah ore masu domin taimakawa zawarawa da marayu, sun bada dauri daurin shinkafa har guda 400, da indomie katan 75, da mangyada katan 12, da turamen atanfa 500 da yaduddukan shadda na mutane 200.
Shugaban ya kara da cewa yawan adadin kudin da aka kashe wajan sayen kayayyakin sun kusa milyan biyu da dubu dari shidda.
Shugaban Izala sheik Abdullahi Bala Lau, ya fadi muhimmancin tallafain harma ga ‘yan gidan yari, inda ya ce wajibi ne a cikgaba da taimaka masu,da kuma yi masu nasiha, zawarawa kuma ba a taimaka masu kawai ba, yakamata a samu wadanda zasu aure su.
Akwai muhimmanci kwarai wajan shigowar al’umma domin taimakawa marayu da ‘yan gudun hijira musamman a wannan lokaci da kasar take cikin wani yanayi.
Your browser doesn’t support HTML5