Dakile Matsalar Shaye Shaye A Jamhuriyar Nijar

Kasancewar jamhuriyar Nijar a tsakanin ksashen dake kusa da arewacin Afirka yasa masu safarar miyagun kwayoyi ke neman hanyoyi na kutsawa cikin kasar domin sayar da su cikin kasar kokuma ketarawa zuwa kasashen magreb ko kuma kasashen larabawa domin ketarawa zuwa kasashen Turai.

A cewar babban alkali mai shigar da kara a babbar kotun binin Konni da sunan gwamnati Malam Musa Haruna, ya ce matasa ne ke shan kwayoyin.

Alkalin ya bayyana cewa “matasa ne ke shan kwayoyin, kuma kasa bata ginuwa sai da matasa domin kuwa, tsofaffi na dogaro ne da matasa, haka kuma kananan yara suma matasan suke dogaro akan su domin su girma su zama matasa, ta dalilin haka ne muke kira ga matasa da su gujema wannan hali na shan kwaya”.

Ya kara da cewa anyi kira da wayar da kan jama’a akan illolin shaye shaye, da safarar miyagun kwayoyi domin matasa su bar wannan dabi’a, kuma a hana masu kawo kwayoyin da masu sayar da su. Matsalar shaye shaye tana hallaka matasa. Kamar wadanda suka sami matsalar tabin hankali a sakamakon shan kwayoyi idan aka yi masu magani sukan sami sauki, amma idan suka cigaba da sha, ko anyi masu maganin basa warkewa.

Ta dalilin haka ne a wannan shekarar aka kama masu sayar da kwayoyi da yawa da kuma masu zuwa wasu kasashe domin su kawo kwayoyi anan kasar, duk wannan kokarine da jami’an ‘yan sanda da jandarmomi suka yi.

Shugaban sufuri na birnin Konni cewa yayi jami’an tsaron na matukar taimaka masu a cikin tashohin da suke daukar fasinja inda yawancin matasan ke boyewa domin aikata wannan mugunyar dabi’a ta shaye shayen kwayoyi.

Yanzu haka dai ‘yan Nijar sun dukufa domin tabbatar da dakile wannan matsalar kamar yadda babban alkali mai shigar da kara da sunan gwamnati ya bayyana cewa zasu gurfanar da duk wanda suka samu da hannu.

Saurari cikakken rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Dakile Matsalar Shaye Shaye A Jamhuriyar Nijar