Babu Wani Dan Najeriya Da Bashi Da Baiwa!

Sojan Najeriya Charles Nengite

A duk irin halin da dan Najeriya, ya samu kanshi to yayi godiya ga Allah. Duk yadda mutun ke tunanin bashi da wata hazakar da zata kai shi, ga wani mataki da wasu suka kai, to ya sake tunani. A kowane lokaci mutun ya karanta jaridu ko kasidu na duniya, zaiga yadda ake bayyanar da irin rawar gani da ‘yan Najeriya, ke takawa a kasashen duniya.

A she kuwa wannan wata damace da ya kamata matasa su tashi tsaye don shiga cikin jerin ‘yan Najeriya, masu bada tasu gudunmawa a duniya. Wani dan Najeriya, Kanal na soja Charles Nengite, ya kafa tarihi a babbar kwalegin hafsoshin soji ta kasar Amurka "U.S War Collage". Ya doke abokan karatun shi mutun dari uku da tamani 380, inda ya zamo na daya.

An bayyanar da hazakar ta shi a shafin kwalegin, da cewar a cikin jerin mutane dake zuwa kwallegin daga kasashe daban-daban a fadin duniya, cikin shekaru talatin da takwas 38, ba’a taba samun wanda ya samu sakamako irin nashi ba. Biyo bayan samun wannan sakamakon yasa ambashi lambobin yabo.

A tabakin shugaban kwalegin Mejo General William Rapp, yace “Sakamakon Mr. Charles, ba shakka shine na farko a cikin jerin kwasa-kwasai da suke gabatarwa na kasa-da-kasa a wannan kwalegin.” Ya kara da cewar lallai ya kamata mutanen kasar Najeriya, suyi fahariya da wannan dan kasar nasu, sannan a kara samun wasu suyi fiye da abun da yayi, domin ya nada yakinin cewar kasar nada wadanda suka fishi.