Albasa Na Maganin Cutar Kansa, Da Kara Yawan Gashi!

Grow It Yourself: Onions Are Nothing to Cry About

Bincike da aka gudanar, ya bayyanar da matukar muhimancin cin albasa ga jikin dan’adam. Dr. Ajobo, likita ne a fanin binciken kwayoyin hallita masu gina jikin da’adam. Ya bayyanar da cewar a iya binciken da suka gudanar, sun iya gano cewar bayan kara kamshin abinci da kara mishi dandano da albasa keyi.

Albasa na dauke da wasu sinadarai da suke maganin cutar kansar ciki, kuma tana dauke da sinadarin bitami C. Ya kara jaddada muhimancin cin albasa, don kara samun lafiya da gujema kamuwa da cutar kansa, haka da maganin hawan jini ga mutane masu dauke da cutar.

Sai yace akwai nau’o’I daban-daban na albasa, kama daga girma, zuwa kala, kamshi da dai wasu abubuwa da suke banbanta su. Amma albasar da tafi dauke da sinadarai masu gina jiki da samun lafiya, itace albasa mai launin Ja. Haka ma yawan cin albasa, na kara lafiya fatar jiki da kara yawan gashi a jikin mutun.