Canje canjen da ya kaddamar bayan da aka bayana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da ya gabata a kasar Nijar shugaba Issoufu Muhammadou, yaba dansa Abba Muhammadou Issoufu, mukamin jami’in kula da harkokin sadarwa a fadar shugaban kasar Nijar.
Sai dai tuni ‘yan kasar ta Nijar, irin su mawallafin jaridar Le Temps, mai zaman kanta Zubairu Sule, suka fara yiwa wannan nadi fassara, yace koda yake dansa ne dan kasa ne doka bata hana bay a nada shi akan wannan matsayi tunda matsayin siyasa ne.
Ya kara da cewa shekaru biyar da yayi a wa’adin san a farko an kashe kudi da dama domin ayi tallar Nijar a koina cikin duniya, yaga an cinye kudin amma ba’a yi tallar Nijar din ba watakila wannan cikas din da ya samu yasa yaga cewa yakamata ya dauki wanda ya yarda dashi yasa ya dauki dansa.
Kakakin gwamnatinkasar ta Nijar Asumana Malam Isa,yace gwamnati bazatayi furuci akan wannan nadi ba.
Sai dai mawallafin na jaridar Le Temps, ya tunatar cewa shugaba Issuofu Muhammadou, da jam’iyyar sa PNDS tarayya, sun sha sukar irin wannan nadi a zamanin da sulke adawa da Gwamnatin Tanja Muhammdou.
A farkon want jiya ne shugaban kasar ta Nijar, ya kori mashawartansa da aka kiyasta cewa sun haura dubu daya abinda wasu manazarta ke ganin alama ce ta rashin gamsuwa da aiyukansu a tsawon shekaru biyar na wa’adin mulkin san a farko, kada yake jam’iya mai mulki ta musata haka.