Tun a shekarun 1950, aka fitar da tsarin sakama duk wata annoba suna a fadin duniya. Musamman idan annobar ta hada da daukar rayukan mutane, ko asarar dukiyoyi. Hakan kuma ya samo asaline a ganin da wasu keyi na idan aka saka ma annoba suna, to mutane zasu lura da irin girman annobar da kuma musifu dake tattare da ita.
Kamar a shekarun baya da suka wuce an samu guguwar iska da ruwa wadda aka sama suna “Hurricane” wadda tayi sanadiyar mutuwar sama da mutane dubu goma 10,000 da asarar dukiyoyi sama da dalla milliyan dari da takwas $108M. Haka a shekarar 2004 anyi wata annoba mai suna “Charley” da ta shafi kasashen kudancin Amurka, da wasu daga cikin jihohin kudancin Amurka, ansamu mutane sama da arba’in da suka mutu sai dukiya da ta kai sama da dalla billiyan goma sha biyar $15B.
Haka a sheakrar 2005, an kara samun wata guguwa da ruwa a yankin kasar Cuba, da wani bangare na kasar Amurka, da aka sama suna “Dean” itama sama da mutane saba’in suka mutu, kuma dukiya ta kai sama da dalla billiyan goma sha biyu. Sai guguwar da aka samu mai suna “Tsunami” itama tayi sanadiyar mutuwar mutane da dama da billiyoyin kudi. Tana kuma cikin ta daya a jerin annobar iskar ruwa da iska da tarihin duniya ba zai taba mantawa da itaba.