Mawakiyar Da Tafi Kudi Cikin Mawakan Kasar Amurka!

Shahararriyar mawakiya “Madonna” ta zamo mawakiyar kasar Amurka da tafi kowane mawaki ko mawakiya kudi a shekarar 2016. Mawakiyar ta samu kudi a wata wakar ta da tayi mai suna “Material Girl” ta zuba zunzurutun kudade da suka kai dallar Amurka milliyan dari biyar da sittin $560M a wajen samar da kwafi na wakar a fadin duniya.

Ta zama mace data samu kudin ta batare da taimakon wani ba, ita dai sananniyar mace ce, a harkar waka da tallace-tallace. Bada jimawa ba ta samu kudi da suka kai dallar Amurka, milliyan dari da saba’in $170M, wanda yanzu haka tana da tsabar kudi da suka kai fiye da dalla billiyan daya da milliyan dari hudu $1.4B

Ta mallaki wasu rukunin gidaje a babban birnin New York, a yankin Manhattan, wanda ba kowa ke iya siyan gida a yankin ba, sai wane da wane. Tana kuma wasu kasuwanci ba kawai a waka kawai ta tsaya ba.