Rundunar sojojin ruwa ta Najeriya ta chafke wasu yan kasar jamhiriyar Benin uku bisa yiwa amfani yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta cikin ruwa.
Wakilin Muryar Amurka a Abuja Hassan maina kaina ya ce hakan na kunshe cikin sanarwa da rundunar ta fitar mai dauke da sanya hanun daraktan watsa labarunta, kwamanda Christian Ezekobe . Hedkwatar sojin ruwan ta ce jami'anta sun damke Ohilmen Agboku, Mr. Penu Daniel, Sule Soka, Dosu Victor da kuma Sodope Okupe dukkanninsu yan kasa jamhuriyar Benin.An kama su dauke da man fetur mai yawa da ake zargin na sata ne cikin jirgin ruwa.
kazalika, rundunar ta kuma cafke Karin wasu yan ta"adda a guda uku a jihar Delta dake yankin Niger Delta. rundunar ta kuma ce ta sami nasarar kama wani jirgin ruwa dauke da durum tamanin na fetur din da aka tace ba bisa ka'ida ba kana ta rugurguza wata matatar mai da ake tace man a sace a karamar hukumar Ayakumuro dake jihar Delta.
Sojojin ruwan sun jaddada kudirinsu na ci gaba da sa ido don kawar da yan ta’addan dake yiwa tattalin arzikin Najeriya Illa ta ruwa da kuma ci gaba da kare yanci da diyaucin Najeriya ta iyakokn ruwanta.