Dubban Matasa Sun Mutu A Kokarin Zuwa Kasashen Turai!

Italy Migrants

Kimanin mutane sama da dubu daya da talatin 1,030 ne suka mutu a makon da ya gabata, a kokarin sun a barin kasashen su zuwa kasashen turai. A ranar Laraba wani jirgin ruwa dauke da mutane, ya nitse cikin teku da mutane da yawa, sai kuma a washe gari Alhamis, wani jirgin dauke da wasu karin mutane sun sake nitsewa, wanda jami’in ‘yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya Mr. William Spindler, ya bayyanar.

Yanzu haka dai akwai sama da mutane dubu dari shidda da sittin da takwas da suke tsare a wani sansanin ‘yan gudun hijira. Daukacin mutane nan sun fito ne daga kasashen kudu da hamada, wadanda suka hada da kasar Najeriya, Gambia, Somalia, da kasar Ivory cost.

Yanzu haka dai kasar Italiya, sun bayyanar da cewar suna dauke da ‘yan gudun hijira sama da dubu dari biya 500,000. An kuma kara bayyanar da hadarin wannan tafiye-tafiye da mutane kanyi, musamman daga kasashen Afrika don zuwa kasashen turai. Domin kuwa mafi akasarin mutane da suke tafiya wadanndan kasashen, basa gane komai illa dai suna fuskantar wata azaba da bai kamata ace sun fuskanta ba, idan sun zauna a kasashen sun na haihuwa.