An gudanar da aikin ciro jaririya a cikin cikin mahaifiyar ta, wata yarinya mai kimanin shekaru goma sha tara 19, ta zama uwa da ta haifi jaririyar da tafi kowane jariri girma a fadin duniya lokacin haihuwa.
Nandini, ta haifi ‘ya mace, wanda sai da aka gudanar da tiyata wajen ciro yarinyar, da keda nauyi na ma’aunin gwada nauyi goma sha biyar 15, a cewar likitan da ya karbi haihuwar Dr. Venkatesh, na asibitin gwamnati da ke garin Hassan na yankin kudancin jihar Karnataka a kasar India, ya bayyanar da wannan jaririyar a matsayin jaririyar da duk kasar India ba’a taba haihuwar jaririya mai nauyin ta ba.
Yace ya kwashe sama da shekaru ashirin da biyar 25, yana aikin likitanci, amma jaririn da yafi kowannen girma da ya taba gani shine, jaririn da ya kai nauyi a ma’aunin nauyi bakwai da dugo biyar 7.5. Yana ganin cewar wannan jaririyar ba wai a kasar India ba, a duniya baki daya ma wannan jaririyar zata zamo wadda tafi kowane jariri girma a duniya a lokacin haihuwa.
Nandini, mahaifiyar yarinyar ita kanta nauyin ta casa’in da hudu ne 94, kana dana da tsawon inci biyar da dugo tara 5.9, kuma an tabbatar da lafiyar uwar da na jaririyar. Likitocin dai sun bayyanar da wannan tiyatar da ya kwashe kusan awa daya anayi, da ban mamaki da suka ga wannan jaririyar mai nauyin gaske.