Meyasa Tsarin Ilimin Kasar Finland Yafi Kowanne Inganci A Duniya?

Masana bincike a fanini ilimi a duniya, sunyi ittifakin cewar dalilin da yasa tsarin ilimi a kasar Finland, yafi na kowace kasa nagarta da inganci shine. A shekaru da dama da suka gabata, tsarin ilimi a kasar Finland, da Australia, sune kasashe da su kafi koma baya a fannin ilimi. Hakan dai yasa kasashen tashi tsaye wajen gano dalilin hakan.

Wasu daga cikin dalilan da suka bayyanar a matsayin umulhaba’isn koma bayan ilimi a kasar shine, yadda tsarin karatu yake na kwashe awowi sama da bakwai 7, a makaranta, da kuma bama yara aikin gida mai yawa. Sun gane cewar a duk lokacin da akace yaro ya kwashe awowi bakwai a makaranta, kuma bayan an tashi makaranta sai su tafi wani aji da ake kira lesin, wanda ake gabatar da shi bayan makaranta, sannan su tafi gida da aikin gida, duk da burin wai su fahimci karatu.

Alkalumma sun bayyanar da cewar wannan shine dalilin da yasa yara basa fahimtar karatu, duk da cewar suna kwashe awowi masu yawa a makarantar. Sun kara da cewar, rashin bama yara damar watayawa a mastayin su na yara, na daya daga cikin dalilan da yasa basa fahimtar karatu. A cewar tsohuwar ministan Ilimi a kasar ta Finland Ms. Krista Kiuru, sun dauki tsarin bama yara damar aiwatar da wasu abubuwa da suke soma ransu, batare da tsara musu yadda zasu gudanar da rayuwar su ta yau da kullun ba.

Hakan na daya daga cikin dalilin da yasa suke fice, don a duk lokacin da yaro yayi ma kanshi zabin abun da yake so, to za’aga cewar abun nan da ya dauko yana da ma’ana da tasiri a rayuwar shi. Hakan wani dalili ne da yake nunama iyaye da cewar, ba wai kawai kai yaro makaranta shine hanyar ilmantar da shi ba, sai an hada da bashi damar amfani da kuruciyar shi, da kuma dubawa don ganin abun da yaro ke so a rayuwar shi, da bashi kwarin gwiwa yadda ya kamata.