Kallon Hotunan Batsa A Waya Na Tattare Da Hatsurra!

Kallace-kallacen hotunan batsa, a wayoyin mutane na tattare da haddurra. Matasa kan iya shiga cikin munanan haddura idan suna da dabi’ar kalon hotunan da basu dace ba. Masana sun bayyanar da wasu matakai da ya kamata matasa su dauka don gujema matsaloli

Mutun na iya shiga cikin hadari, idan yana amfani da wayar hannu, don kallace-kallacen hotuna ko bidiyo na batsa. A cewar wasu masu bincike a harkokin tsaro, akwai manhajoji sama da dari 100, wadanda aka kirkire su don satar data da kudin waya.

Wadannan manhajojin zasu fi samun galaba akan tsofaffin wayoyin android, domin suna nan da yawa ba sai mutun ya biya ba. Idan har masu satan data suka saci datar mutun, kuma suka aiwatar da wani abu na rashin gaskiya, idan akazo bincike za’a ga wata lamba da ake kira “IP” wanda zata bayyanar da cewar mutun ne yayi wannan laifin. Don haka matasa sai a kula.