Kasashe Da Su Kafi Cin Bashi A Duniya!

Global Finance

A jiya ne akayi bukin ranar masu cin bashi a duniya. Hakan yasa mun duba kasashen duniya da su kafi cin bashi a fadin duniya. Da yawa da ga cikin kasashen nan da suke da dinbin bashi, suna fama da talauci a cikin su.

Don haka sai mutun yayi tambaya, wai shin ina kudaden da suke ciyowa bashi suke zuwa? Za kuma aga cewar duk wadannan kasashen suna fama da matsalolin tattalin arziki. Hukumar lamuni ta duniya, ta bayyanar da kasashe da sukafi cin bashi a duniya.

Kasar Japan, itace kasa ta farko, sai kasar Greece, haka kasar Italy, tazo ta uku. Kasar Jamaica, na biye, sannan kasar Lebanon, kasar Eritea, suna cikin jeri. Kasar Portugal, itama tana ciki, sannan kasar Cape Verde, tazo ta takwas, kasata tara kuwa itace kasar Bhutan, sai kasar da tazo ta goma itace kasar Ireland.