Motar Kamfanin "Google" Mai-Tuka Kanta, Zata Kawo Raguwar Hadari

Google car-5

Kamfanin google sun kara jaddada aminci da nagartar motar da suka kera, da kuma bada tabbacin cewar motar zata samar da yanayin da baza’a dinga samun yawan hatsari akan tituna ba.

Ita dai wannan motar mai tuka kanta batare da wani ya tukataba, an tanadar mata da na’urori da zasu dinga nuna mata hanya, hakan yasa idan mutun na ciki zai iya yin wani aikin shi, batare da ya damu da yadda tuki yake gudana ba.

Hasali ma sun kara da cewar, ita dai wannan motar mutane kan iya maida ta kamar gidan su, a loacin da suke tafiya, haka mutun zai iya yin aikin ofis a dai-dai lokacin da motar ke tafiya batare da wata damuwa ba.

Duk lokacin da motar take tafiya da kanta, babu wani abu da zai shiga gaban ta, batare da ta aiwatar da wani abu da ya dace ba, na kokarin kare kanta da mutanen ciki. Hakan yasa baza a dinga samun yawan mace mace ba a sanadiyar hatsari da ake samu akan tituna.