Wasu mutane kanyi wasu abubuwa a wajajen aikin su, wanda hakan yake kara samar musu so da kauna a wajajen shugabanin su da sauran abokan aikin su. Haka kuma wadannan abubuwan suna kara basu damar samun nasarori da yawa.
Kowane mutun na da irin tashi baiwar da daukaka da Allah yayi mishi, amma dokoki da tsare-tsaren ma’aikata na bada dama don cinma duk wata nasara a wajen aiki. Duk mutumin da ya dauki buri akan abun da yake so yayi a wajen aiki batare da bata lokaci ba, idan ya dukufa cikin awowin aiki ya ga cewar ya samu kamala duk abun da yasa a gaba, to zai samu karbuwa a wajen aiki.
Haka mutun da bai damu da ya dinga tambaya akan abun da bai sani ba, shima ba zai zama wani abu a gaba, an tabbatar da cewar duk mutumin da yake tambaya, to babu shakka zai lakanci aiki sosai, haka kuma idan kaga mutun baya tambaya, to lallai yanayi abu daya iri daya babu canji. Hakan kuma na kara dankwafar da basira da samar da rashin jituwa da sauran abokan aiki.