A karon farko wasu matasa a jami’ar kimiyya da fasaha ta kasar China, dake gudanar da wani bincike, sun kirkiri mutun mutumi da yafi kowannen kama da mutun a duniya, na wata mace da suka bama suna Jia Jia. A satin da ya gabata ne akayi bukin kaddamar wannan “Robot” din.
Ita dai mutun mutumin da aka sama suna Jia Jia, tana magana kamar yadda mutane ke magana, sai dai duk abun da take fada yana daga cikin abubuwan da aka saka a cikin kwakwalwar ta. Wani abun ban mamaki da wannan yarinyar shine, idan mutun na daukar ta hoto zata gaya mishi cewar ya dena daukar ta hoto, amma bata iya banbance na miji ko mace. Tana kiran kowa da sunan mace ne.
Wasu daga cikin abubuwan da take iyayi, sun hada da gaida mutun tana kuma amsa gaisuwa, sannan za tace ma mutun taya zan taimake ka? Tana gaisawa da da girgiza hannun mutane, tana dariya, haka ma tana rungume mutun. Aikin kera wannan robot din ya dauke su tsawon shekara daya suna aiki a kai. Haka sun kashe kimanin kudi da suka kai dallar Amurka dubu hamsin $50,000 dai-dai da naira milliyan goma.