Wata yarinya da ba’a bayyanar da sunanta ba, mai kimanin shekaru goma sha tara, ‘yan yawon shakatawa ta mutu sanadiyar jirgin kasa ya bugeta. Ita dai wannan yarinyar tana tare da sauran mutane, inda take kokarin daukar hoton kanta da ake kira “Selfie” a turance, mutanen da ke kusa da ita sunyi kokarin jawo hankalin ta da cewar ga jirgi nan tafe, amma bata kula suba.
A cikin kokarin ta na ganin tayi hoto mai kyau, da kuma daukar wani bangaren jirgin cikin hoton ta, koda jirgin ya kawo inda take bata matsa ba, jirgin ya bangaje ta wanda ta mutu a nan take. Hakan ya faru ne a wani gari da ake kira Guandong, a yankin kudancin kasar China.
An bayyanar da wannan a matsayin wata annobar zamani, da tayi dabaibayi ga matasa na wannan lokacin. Domin kuwa sau da dama matasa kanyi amfani da wayoyin su wajen daukan kan su hoto ko dai mutun daya ko kuma cikin taro. Don haka ana kara jawo hankalin matasa da su kaurace ma wannan dabi’ar don samar ma kansu zaman lafiya.