Garuruwan Da Su Kafi Samun Yawaitar Baki A Fadin Duniya

New York

A cigaba da kawo jerin garuruwa da su kafi samun baki a 'yan yawon bude ido da shakatawa a fadin duniya. Garin New York a kasar Amurka, shine gari na 8, da yawan mutane milliyan 12.2, suke ziyarta a shekara. Garin Istanbul na kasar Turkey, dake da milliyan 11.9, haka garin Kuala Lumpur, na kasar Malasia, da milliyan 11.6, sai garin Antalya, a kasar Turkey, da mutane milliyan 11.5, haka suma garin Dubai a yankin kasashen daula larabawa nada yawan mutane da suka kai milliyan 11.4.

Haka garin Seoul a kasar South Korea, sun samu adadin mutane da suka kai kimanin mutane milliyan 9.4, sai babban birnin Rome, a kasar Italy da suka samu mutane milliyan 8.8, suma garin Taipei, a kasar Taiwan sun samu mutane sama da milliyan 8.6, kana garin Guangzhou, a kasar China, sun kai kimanin mutane milliyan 8.2.

Garin Phuket, a kasar Thiland da suka samu kimanin mutane milliyan 8.1, haka suma garin Miani a jihar Florida ta kasar Amurka, sun samu mutane da suka kai milliyan 7.3, garin Pattaya a kasar Thailand ba’a barsu a baya ba sun samu mutane sama da milliyan 6.4, Su kuwa garin Shanghai a kasar China sune cikon gari na 20 da su kafi samun baki ‘yan ziyara a fadin duniya.