‘Yan Najeriya na kara yawa a cikin klob din Arsenal, yanzu haka dai ‘yan Najeriya dake buga ma kungiyar Arsenal wasa sun kai matasa takwas. Marc Bola, mai shekaru 18, ya saka hannu akan kwantiraki da gungiyar ta Arsenal. Shi dai matashin mai ruwa biyu da Ingila da Najeriya, ya taka rawa wajen ganin ‘yan wasa yan kasa da shekaru 18 sun yi nasa a wasan zakaru da suka yi nasara.
A lokacin wannan wasan ne yasa shugaban klob din Arsenal, Wenger yaga cewar akwai abun da kungiyar zata karu da shi idan har suka dauki hayar dan-wasan Bola. A cewar kungiyar ta Arsenal da suka rubuta a shafin su na yanar gizo. "Kowa ya kosa dan wasan Bola, ya shigo kungiyar don ya bada ta shi gudunmawar, suna kuma sa ran ko dai ya buga wasan gefe ko ya zama mai tsaron baya".
Shi dai mai tsaron bayan gida Bola, ya nuna kwarewar shi a cikin fili, yanzu haka dai zai cigaba da bada tashi gudunwar a cikin jerin ‘yan wasa masu shekaru 21. Cikin jerin sunayen ‘ya Najeriya da ke buga ma kungiyar Arsenal, wasa, sun hada da Alex Iwobi, Chuba Akpom, Kelechi Nwakali, Samuel Chukwueze, Asisat Oshoala, Chiori Johnson da Tolaji Bola.