Dr. Suraiya, Na Ganin Kula Da Lafiyar Dabbobi Kamar Kula Da Lafiyar Mutu Ne!

Likita Suraiya Mansur

Dr. Suraiya dai likita ce mai kishin kasar ta Najeriya, inda ta baiyyana cewa bayan ta kamala digirin ta na biyu datake yi yanzu a Texas A&M University, zata cigaba da karatun ta har digirin digirgir duka a bangaren ilimin lafiyar al’umma. Toh bayan nan tana da burin komawa kasar ta najeriya, don bada nata gudun wajen cigaban kasa, mussamman akan cututtukan da mutane ke dauka daga dabbobi (Zoonotic Diseases).

Ta bayyana cewa mutanen amurka basu fi mutanen Najeriya kokari ba, suna kishin kasar su ne sosai kuma sun dauki daddobin su tamkar ‘ya’yan su wajen kula da lafiyar su abin da a gida Najeriya ba’a dauka da mahimmanci ba sosai.

Shawarar da take bawa matasa musamman ‘ya’ya mata shine su mai da hankulan su, su nemi ilimi yanda zasu taimaki rayuwar su, su tallafawa iyayen su da mazajen su, su bawa yaran su tarbiyya ta gari yanda za’a samu cigaban al’umma gaba daya. Masu iya Magana sun ce ilimin ‘ya mace tamkar ilimin al’umma ne baki daya.