Liam Murphy, yaro ne mai shekaru 13, wanda yazo da wata sabuwa. Shi dai matashin ya shigar da karar iyayen shi a kotu, inda ya bukaci su biyashi tara na kudi da suka kai yawan dallar Amurka milliyan $2M dai-dai da naira milliyan dari hudu N400,000,000.
Dalilin wannan rayon na kai iyayen shi kara shine, iyayen sun haife shi da jan gashi. Wanda yake cewa ai sun san da cewar idan suka haife shi zai gado su da jan gashi, don haka mai yasa basu fasa haihuwar shi ba. Domin yanzu wannan gashin baya barin shi jin dadin rayuwar shi.
Yace su biya shi dallar Amurka $1.35M na sashi cikin damuwa da wannan jan gashin kanshi ya saka shi ciki, sai su biya shi dalla milliyan dari takwas $800,000M na saka shi cikin halin da yake ci wanda yake ganin kanshi a matsayin mara lafiya, idan aka hada shi da sauran yara masu kalan bakin gashi. Don yana ganin hakan yasa shi rasa jin dadin rayuwar shi.
Yaron ya gayama ‘yan jarida bayan fitowa daga kotun cewar “Rayuwa shi ta shiga matsanancin hali, an sha gayamun cewar nafito daga jinsin dangin dake da hadari. Mutane da dama suna kira na da wasu irin sunaye na daban da suka hada da abu marasa kyau, duk wannan ya farune a sanadiyar iyaye na basu gujema haihuwa ta ba, yanzu haka suna da masaniyar sakani cikin rayuwa mai kunci, wanda yanzu son zuciyar su ya kaisu ga haihuwa ta.”
Lauya mai kare yaron, ya bayyana dacewar yaron yana da magana ta dubawa, wanda yake da yakinin cewar za suyi nasar, domin kuwa iyayen shi sun saka shi cikin wani hali na kunci. Wanda idan da basu haife shi da wannan jan gashin ba to da bai samu damuwa a rayuwar shi ba baki daya.