Hukumar binciken manyan laifufuka ta kasar Amurka “FBI” sun samu damar bude wayar dan ta’adda nan Syed Farook, da matar shi Tashfeen Malik, da suka kai hari a garin San Bernardino, a watan Disamba, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 14.
Dama dai tun bayan kai harin akaita takaddama tsakanin gwamnatin Amurka da kamfanin na Apple, da su basu lambobin da za suyi amfani da su wajen bude wayar don ganin duk wasu abubuwan sirri na dan ta’addan. Amma kamfanin sunki wanda suka bayyanar da hakan a matsayin karya hakkin dan kasa.
Yanzu dai haka wannan fadan zai sake daukan sabon salo, inda ma’aikatar shari’a take ganin wannan ya saba dokokin hakkin dan kasa. Yanzu dai haka kamfanin na Apple ya bama abokan hurdan shi tabbacin cewar zasu kara azama wajen ganin sun inganta wayar su da babu wani da zai iya bude ta balle har ya dauki bayanan su na sirri. Sun kara da cewar zasu bama duk wasu jami’an tsaro hadin kai da duk ya kamata wajen cinma burin tsaron kasar.