Hukumar CAF Ta Ragema 'Yan Wasan Najeriya Maki 3!

Hukumar kwallon kafar kasashen Afrika (CAF), ta rage ma ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya maki, a wasan da ake bugawa na zakaru don shiga gasar wasan cin kofin duniya na kasashen Afrika a karo na 31, wanda kasar Gabon, zata dauki bakonci a shekara mai zuwa 2017.

‘Yan wasan kasar Chadi, sun bayyanar da cewar baza su samu damar zuwa kasar Tanzania, ba don cigaba da gasar, bisa ga wasu dalilai na rashin kudi. A dalilin haka yasa hukumar ta aiwatar da hukuncin ragema ‘yan Najeriya maki, hukumar dai ta kara da cewar bisa ga dokar hukumar tsari na 61, wanda yace “Idan aka samu wani klob ya fita daga gasa wasan zakaru da aka tsara a cikin rukuni, duk wani sakamako a soke shi” haka kuma wasan da kasar ta Chadi zasu buga na rukunin G shima an soke don haka sakamakon baza’a yi amfani da shi ba.

Kasar Egypt dai ita ke jagoranci da maki 4, sai kasar Najeriya na binta da maki 2, haka kasar Tanzania nada maki 1. Hukumar ta kara da cewar a yarjejeniyar da aka cinmma a ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 2015, da cewar duk rukuni da aka samu wani klob ya fita, to klob din da ke da rinjaye a rukunin zai zama zakara. Yanzu haka dai anci kasar Chadi tarar kudi da suka kai dallar Amurka $20,000 dai-dai da naira milliyan hudu N4,000,000. 'Yan wasan Najeriya dai zasu hadu da aboka karawar su na kasar Egypt a yau Talata.