Dakaraun Iraki, tare da goyon bayan mayakan kurdawa na Peshmerga, sun kaddamar da wani farmaki na kwato birnin Mosul inda ‘yan kungiyar ISIS suka yi karfi.
A safiyar yau, wasu birged guda biyu daga shiyya ta 15 ta rundunar sojojin Iraqin da Amurka ta horas, sun fara farma wasu kauyuka 6 da ‘yan ISIS suke rike da su a kudu maso gabas da Mosul.
Cikin dakarun har da wasu mayaka na kabilu ‘yan mazhabin Sunni, abinda wasu kwamandojin ‘yan Peshmerga su ka ce suna da muhimmanci wajen rike garuruwan na ‘yan sunni.
Wani kwamandan dakarun Kurdawa, Janar Najat Ali, mai kula da yankin Makhmour ya fadawa muryar Amurka cewa yau sojojin Iraki sun fara dannawa kauyukan.
Janar din ya kuma ce, dakarun na Peshmarge ba sa shiga cikin fadan da akeyi kai tsaya saboda ana yin shi ne garuruwan ‘yan sunni, amma su na ba dakarun Iraki bayanan sirri akan kauyukan.