Wani Dan Najeriya Ya Kara Samarma Najeriya Daraja A Duniya

Muntaqa Umar Sadiq

Muntaqa Umar Sadiq, matashi dan Najeriya da ya samu lambar yabo mai girma a duniya na kungiyar “The World Economic Forum” wannan wata kungiyace da manyan mutane na duniya ke ciki. Kungiyar ta karrama Muntaqa, a matsayin wanda ya lashe lambar girmamawa na shekarar 2016 Young Global Leader.

A tabakin shugaban kungiyar na duniya Mr. Klaus Schwab, Muntaqa ya cancanci wannan girmamawa, saboda irin aiki da yayi ma jama’ar shi a kasar shi ta Najeriya, a matsayin shi na mutun da yake da sha’awar taimaka ma mutane a fannin kiwon lafiya.

A tsarin wannan kungiyar sukan duba mutane da suke taimakon al’umah a duniya don basu dama da karin karfin gwiwa wajen taimakama mabukata, sukan zakulo mutane da suke ‘yan shekaru kasa da 40. Muntaqa dai yayi karatun shi na digirin farko a kasar Ingila, a bangaren kiwon lafiya. Wannan wata babbar damace da ta isa kasashen Afrika, musamman ma kasar Najeriya da suka samu wannan lambar yabon a karon farko.