Dr. Mubarak Muhammad Tukur, matashi mai son karatu matuka. Ya tashi a garin Kano na arewacin Nigeria. Ya halarci makarantar firamari ta Bayero University Staff School, sannan yayi makarantar Crescent International Secondary School. A wannan lokacin burin shi shine ya zama injiniya saboda yana son lissafi. Amma kafin ya rubuta jarrabawar JAMB a shekarar karshe ta sakandire sai ya canza ra'ayin shi. Saboda la'akari da yayi na karancin likitoci a asibitocin Najeriya, sai yasa himma wurin zama likita. A shekarar 2003 ya sami gurbin karatu a jami’ar Bayero dake kano. Ya samu damar gama digiri na farko a shekara ta 2011. Inda ya zama cikakken likita.
A shekarar 2012, ya samun damar karo karatu a kasar waje. Don yayi digiri na biyu a bangaren public health ke nan lafiya jama’ar karkara, a jami'ar Texas A&M University dake jihar Texas, kasar Amurka. Bayan an zabe shi a cikin wadanda suka cancanta sai ya rubuta jarabawar gwajin turanci da lissafi na TOEFL da GRE wanda ya bashi damar samun gurbi a wannan jami’ar. A yanzu haka yana digiri na biyu wanda zai kammala a karshen shekarar 2016.
Rayuwa a Amurka, garin da yake bai yimi shi wahalar sabawa ba, saboda yana tare da mutanen Najeriya, wadanda su kayi dacen samun wannan damar ta karo karatu kamar shi. Gashi kuma mutanen garin sun iya saukar baki. Kuma yanayin garin yana kama da na arewacin Najeriya. Duk da cewa karatun yana da wahala, ya samu malamai masu taimakawa dalibai da duk abinda zai amfane su.