Shugabanni Kasar Amurka Da Su Kafi Karfi A Tarihin Kasar

Tarihin kasar Amurka baya taba cika, batare da zayyano wasu daga cikin tsofaffin shugabanin kasar. Anyi amfani da wasu alkallumma wajen bayyanar da tsohon shugaba Amurka da yafi karfi a zamanin shugabancin shi. Alkaluman kuwa sune shugaba da yafi dadewa a ofis, da wanda yafi yawan amfani da karfin shugaban kasa wajen aiwatar da wasu abubuwa, haka wanda ya gabatar da wasu tsare tsare da suka shafi hurda da kasashen duniya, kana da shugaba da yayi yaki da yawa, sai shugaba da yafi nada alkalan kotun koli.

Tsohon shugaban Amurka Franklin D. Rooservelt, shine shugaba da yafi amfani da karfin mulki wajen aiwatar da dokoki da suka kai 3,721, ya kuma yi mulki na tsawon shekaru 12, ya kuma nada alkalan alkalai na kotun koli haka kuma ya zama jagoran yaki a lokacin yakin duniya na 2. Duk ire-iren abubuwan da yayi a zamanin shi, yasa ya zama tsohon shugaban Amurka da yafi kowannen karfi a tarihin kasar.

Tsohon shugaba George Washington, kuma shugaban kasar Amurka na farko, bayan samun 'yanci daga hannun turawan mulkin mallaka na Ingila, ya zamo tsohon shugaban kasar na 2 mai karfi. A matsayin shi na shugaba na farko ya nada alkalan alkalai na kotun koli guda 10, a tsawon mulkin shi na shekaru 8, haka ya saka hannu a yarjejeniyar kasuwanci da kasar Ingila.

Shugaba na 3 kuwa cikin tsofafin shugabannin kasar Amurka masu karfi shine Woodrow Wilson, ya zama shugaban canji wanda ya saka hannu akan dokoki 1,803, haka kuma ya samar da kyakkyawar danganta tsakanin kasa-da-kasa da kasar Amurka. Ya jagoranci kasar baki daya tsawon lokacin yakin duniya na 2.