Cutar "Zika" Kada Ta Tsoratar Da 'Yan-Wasa Ko Masu Kallo A Brazil

Hukumar lafiya ta duniya “WHO” tayi kira da cewar ‘yan wasa na duniya da ma’abota kallon wasanni kada su ji wani tsoro game da zuwa kasar Brazil, don yin wasa ko kallon wasa, bisa dalilin tsoron cutar “Zika” shugaban hukumar Margaret Chan, ta bayyana hakan.

A lokacin da ta kai wata ziyara a asibitin IMIT a yanki arewa na kasar Brazil, ta kara da cewar gwamnatin kasar Brazil din, nayi kuma zata cigaba da kokari wajen magance matsalar kamun lokacin da za’a gudanar da wasan a watan Augusta na wannan shekarar 2016.

Tace duk da cewar wannan cuta tana da matukar hadari musamman ma ga yara kanana. Yanzu haka dai a fannin likitanci sun maida hankali wajen ganin an kawo karshen wannan cutar da ma wasu masu kama da ita. Tace wannan shine lokacin da ya kamata mu hada kanmu waje daya, don yakar duk wani abu dake kokarin raba kawuna kan mutane a fadin duniya.